DAWO DA SARKI SANUSI: Sakataran Yada Labaran  Masarautar Kano Yayi Murabus

Daga SHEHU YAHAYA

Biyo bayan Dawo da Sarkin Sanusi kan sarautar Masarautar Kano Wanda gwamnatin jihar Kano tati, Sakataran Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya ajiye aikinsa a jiya.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa, yace Bisa kashin kansa

“A matsayina na Babban Sakataran yada labarai  a Masaratar Kano daga yau nayi Murabus daga wannan mukami”

“Ina rokon Allah yasa haka shine mafi alheri ga Mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero”

“Haka kuma muna yin fatan alheri ga Masarautar Kano da al’umar jihar Kano da suka bada gudunmawa da Soyayyarsu da hadin kansu a lokacin da Mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero yayi ya gudanar da mulkinsa” 

Leave a comment