Gwamnatin Tarayya Zata Fara Allurar Sankaran Mahaifa A Kaduna 

DAGA SHEHU YAHAYA

Gwamnatin Tarayya da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kaduna ta zata  Fara gudanar da  Allurar Sankaran Mahaifa ga mata Yara a fadin jihar Kaduna Baki daya.

Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin Babban jami’i a ma’ aikatar lafiya ta jihar Kaduna  Aliyu Alhassan a wata zantawa da Yayi da manema labarai Jim kadan bayan kammala Taron Masu ruwa da tsaki a harkar lafiya daga Kananan hukumomin jihar 23 tare  da kungiyayi da hukumomin lafiya da ke jihar.

Alhassan Wanda shine Sakataran Lafiya na Karamar Hukumar Makarfi yace, gwamnatin tarayya da haxin gwiwar gwamnatin jihar Kaduna tare qungiyar lafiya ta Duniya (WHO) suka dauki nauyin allura ga mata Yara ‘yan shekara 8 zuwa 19 Domin kaucewa fadawa hadarin kamuwa da cutar wacce take illata rayuwar mata yayin da sukayi aure.

Yace  gwamnati ta ware mako mai zuwa Domin fara gangamin fara Allurar a kananan hukumomin jihar 23 Wanda  daga Bisani  za’a ci gaba da gudanar da Allurar a sauran asibitocin gwamnatin Dake jihar Kuma kyauta.

Ya kara da cewa “Ita kansa wata abace Dake boye a cikin Mahaifa Wanda mutum ba zai iya sanin yana da ita ba Wanda ba za’a tashin saninta ba sai anyi gwaji. Alhamdulillahi yanzu  an fito da rigakafin kamuwa da cutar Wanda za’ayi wa mata daga shekara takwas zuwa shekara Sha tara saboda a kare su daga kamuwa daga Wannan cutar  kamin suyi aure su fara saduwa da mazansu  Domin tana yaduwa ne ta wurin saduwa”

“Yanzu Shiri Yayi Nisa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihar da haxin gwiwar kungiyar lafiya da Duniya ( WHO) wanda Nan sati mai zuwa insha allah za’a fara gangamin fara Allurar kananan hukumomin jihar Kaduna ” 

Akan Hakan, jami’in ya buqaci daukacin al’ummar jihar Kaduna da su fito su rungumi Shirin allurar rigakafin Wanda gwamnatin tarayya ce zata dauki nauyinta, yana mai cewa allura ce da zata taimaki rayuwar mata Nan gaba.

Leave a comment