Burina Jami’ar Al-Qalam Tayi Gogayya Da Jami’oin Duniya…. Inji Farfesa Garki

 Shugaban Jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina Farfesa Shehu Ado Garki, ya bayyana cewa Jami’ar tana daga cikin sauran jami’oin kasar nan da suke bayar da gudummawa wajen bunkasa harkar ilimi a fadin kasar nan Wanda hakan ya sanya mahukunta Jami’ar Suka dukufa  wajen Kara inganta Jami’ar ta bangarori daban-daban.

Farfesa Ado Garki, ya kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba Jami’ar Al- Qalam zata yi gogayya da sauran jami’oin duniya wajen koyarda ilimin kimiyya da fasaha.

Yace” Babban burina shine Al-Qalam ta zama jami’a kamar sauran jami’oi masu koyar da ilimin kimiyya da fasaha haka kuma ta zama tana gogayya da sauran jami’oin duniya insha Allah ”

Ya kuma bayyana cewa Jami’ar Qalam ba ilimin addinin musulunci kawai take koyarwa ba; harda sauran kwasa-kwasan Da suka shafi harshen Hausa Da turanci Da ilimi koyarwa Da kuma kimiyya da fasaha inda yace   ba jami’ace ta musulmi Zalla ba harda wadanda ma ba musulmi ba suna karatu cikinta, a cewarsa, suna bayar Da tarbiyya irin ta musulunci.

Da yake bayani dangane da halin da Jami’ar take ciki, farfesa Garki Ado, ya ce” lokacin da na karbi shugabancin wannan jami’a kwasa- kwasai guda hudu akeyi amma cikin ikon Allah yanzu muna da kwasa-kwasai guda 18 kama daga darrusan kimiyy da turanci da Hausa da koyar da ilimi koyarwa da sauransu Wanda kuma hukumar kula da jami’oin kasar nan NUC ta bada izinin koyar da guda 13 na dindin-din sauran kuma na Wucin gadi ne Wanda cikin wannan watan Zasu zo su duba suka gani kamin Su bada izini na din-din-din. 

Da yake bayani dangane da kula da lafiyar daliban jami’ar, Farfesa Shehu Ado Garki, yace ” mun tanadi dakin kula da lafiyar dalibai harda ma mata masu juna biyu Wanda idan mace haihuwa ta kamata zata iya haihuwa acan, hak kuma mun tanadi injinan samar Da wuta domin koda an dauke wutar lantarki; haka kuma mun gina rijiyar burtsa-tsai domin Samar da ruwan sha mai kyau saboda haka munyi bakin kokarinmu wajen ciyat Da jami’ar gaba.

Akan hakan ya bukaci daukacin daliban Jami’ar da su tabbatar da cewa sun bi dokokin Jami’ar domin ganin sun samu abin da kawosu jami’ar.

Leave a comment