Boko Haram Ta yi Safarar ‘Yan Matan Dapchi Zuwa Kasar Nijar

Rahotanni sun bayyana cewa An yi safarar rabin ‘yan matan makarantar Dapchi da kungiyar Boko Haram ta sace a makon jiya a jihar Yobe ta Nijeriya zuwa Jamhuriyar Nijar.
Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust, cewa, kungiyar Boko Haram ta raba matan gida biyu, in da ta ajiye kashi daya a garin Tumbum Gini da ke karamar hukumar Abadam a jihar Borno a Nijeriya, yayin da ta yi amfani da jirgin ruwa wajen safarar kashi na biyu zuwa wani kauye da ke garin Duro a Nijar.
Rahotanni na cewa, tsagin mayakan Boko Haram karkashin jagorancin Musab Albarnawi ne ya sace ‘yan matan da yawansu ya kai 110 a ranar Litinin da ta gabata a Yobe kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatar da adadinsu.
Gwamnan jihar yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya dora laifin sace daliban akan janyewar dakarun sojin kasar daga yankin, amma rundunar sojin ta musanta haka.
Gwamnan jihar Borno da ya kai wa Gaidam ziyarar jaje, Kashim Shettima ya ce, sace daliban ya tuna ma sa da sace ‘yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014.

Leave a comment