An Kashe Mutum 1 An Yi garkuwa Da 6 A Birnin Gwari

Rohotanni daga jihar Kaduna sun tabbatar da cewa sa’o’I kalilan bayan da wasu ‘yan Bindiga suka yi garkuwa da matan Aure guda 3 da sanyin safiyar yau dinnan a kauyen Maganda da ke a kan titin Birnin Gwari zuwa Funtua, an sake yin garkuwa da wasu mutane 6 a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
Ko a ranar Assabar da ta gabata ma an yi garkuwa da wasu mutane da misalign karfe 9 na safe a yayin da wadanda abin ya rutsa akansu ke tafiya a cikin Motar haya.
Shugaban kungiyar Direbobi ta Najeriya wato NURTW da ke a Birnin Gwari ya tabbatar da hakan inda yake cewar an samu fasinja 1 da ya mutu sakamakon yadda Direban Motar ya saki hanya a yayin aukuwar lamarin.
Matsalar tashin hankali da garkuwa da mutane dai ba bakon abu ba ne a tarayyar Najeriya musamman a yankunan Arewa ta tsakiya da kuma Arewa masu yammaci, inda a baya-bayan nan aka sha samun labarai na masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna da kuma barayin shanu a jihar Zamfara.
A makon da ya gabata ma an samu labarin wasu ‘yan Bindiga da suka kama tare da yin garkuwa da wani Injiniyan kamfanin gine-gine dan asalin kasar Syria a jihar Sokoto, a yayin da suka kashe jami’an ‘yan sandan da ke aiki tare da shi su uku.

Leave a comment