Za’a Hana Sha Da Sayar Da Barasa A Zaria

An samu tashin hankula da fargaba a Sabon garin Zaria dake jihar Kaduna a ranar alhamis bayan da gwamnatin jihar ta ce zata gabatar da wani kudiri da zai hana sha tare da sayar da barasa.

Jin wannan kudiri na gwamnati hakan ya faru ne a karamar hukumar Sabon garin ya kawo fargaba ga a’lumma.

Sabon garin dai yanki ne da ke dauke da al’umomi da dama, tare da yawan otel-otel da masu sayar da barasa.

Jin haka ke da wuya sai masu harkar otel-otel ta hannun lauyansu Mr Daniel Peter ya ce kananan hukumomi a Nijeriya na da ‘yancin bada umarnin hana sha tare da sayar da barasa, inda yake cewa gwamnati bata da hurumin hana sayar ko shan da barasa.

Ya kara da cewa a cikin kudirin a sashi na 5 da 6 ya bayyana karara cewar ya hana sha da sayar da barasa.

Leave a comment