Karamar Hukumar Kibiya Ta Tallafawa Masu Tabin Hankali

A kalla masu tabin hankali guda 40 ne suka amfana da shirin kula da lafiya na Karamar Hukumar Kibiya dake jihar Kano, wajen basu magunguna domin kula da lafiyarsu.

A zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan ya karbi lambar yabo daga kungiyar ‘yan jarida ta Arewa, shugaban Karamar Hukumar Kibiya Alhaji Alkassim Abdullahi Shike, yace Karamar hukumarsa tana daukar dawainiyar kula da lafiyar masu tabin hankalin wajen biya musu kudadan magani har sai sun samu lafiya, inda yace da yawan masu tabin hankali a Karamar Hukumar sun warke.

Shugaban ya kara da cewa, ganin yadda suma masu tabin hankalin suna da hakki a gwamnatinsa, hasalima, da yawansu marasa galihu ne, hakan ya sanya suke tallafa musu.

Yace “Duk wani mai tabin hankali da muka samu labarinshi muna daukarshi zuwa asibitin masu tabin hankali dake Dawanau domin basu kula ta musamman har sai sun samu lafiya kana mu dawo dasu gudajensu, yanzu haka mu kai masu tabin hankali 40 asibiti Wanda yanzu duk sun samu lafiya sun warke.

Alhaji Alkassim Shike, yace karamar hukumar Kibiya ta himmatu wajen binkasa harkar lafiya a fadin karamar Hukumar ta fannin gyara asibitoci da dakunan shan magani dake sassa daban -daban a cikin karamar hukumar.

Rahotanni sun nuna cewa a kananan hukumomi 44 dake jihar Kano, Karamar hukumar Kibiya itace kan gaba wajen bunkasa harkokin kiwon lafiya wanda hatta kananan hukumomi makwabta suna amfana da shirin ta na kula da lafiyar al’umma, lamarin da ya sanya kungiyar na ‘yan jarida suka karramashi da lambar yabo ta musamman.

Sai dai, shugaban, yace suna fuskantar kalubale ga masu tabin hankalin musamman bayan sun samu sauki an dawo dasu gida.

Yace ” matsalar da muke fauskanta shine bayan an sallamo su daga asibiti akwai magunguna da likita yake umartasu dasu rinka sha wanda a duk wata basa wuce naira dubu biyu (#2000) ba Amma sai ka tarar an kasa siya a saboda wanda karama hukuma ba zata iya daukar wannan ba, wanda wasunsu daga baya sai su dawo cikin haukar da tuburan.

“Saboda haka yanzu mun fito da wani tsari na cewa bama daukar dawainiyar duk wani mai tabin hankali sai munyi yarjejeniya da iyayensu cewa idan suka samu lafiya zasu ci gaba da saya musu magani bayan sun warke, domin ragewa karamar hukuma asara da kuma tabbatar da sun warke gaba daya” inji Alkassim Shike.

Leave a comment