Shekara Daya Na  Gwamna Uba Sani   Alheri Ne Ga Al’ummar Jihar Kaduna –  Injiniya Yero





Daga Rabiu Haruna Dankani,  Kaduna

Shugaban hukumar kula da kwangiloli da kuma tsarata na jihar K aduna ( KADPPA) Injiniya Sunusi Aminu Yero,  ya bayyana cewa Shekara Daya na   gwamnatin  Sanata Uba Sani  a Jihar Kaduna alheri Ne ga Al’ummar Jihar  duba da yadda aka shimfida ayyuka daban- daban  a fadin jihar Baki Daya.

Injiniya Yero ya kara da cewa tashin farko mai girma gwamna ya kira wadanda  suke ganin an saba masu domin ganin asama masalaha domin a gudu tare a tsira tare da  dukkansu sunyi na’am da wannan tunanin da mai girma gwamna yayi wanda haka zai kawo nasarori  da kuma shawarwari masu amfani.


Shugaban  yace duk da Dimbin bashin da gwamnatin Uba Sani tasamu bai hanashi aikin da yasa a gaba domin yayi aikin azo agani a jihar Kaduna musamman abun da ya shafa Ginawa da sabunta kananan asibitoci a kananan  hukumomi daban daban,; Gina hanyoyi a birane da karkara ; gyaran makarantu da gina sabbin azuzuwa  da jajircewa domin ganin tsaro ya inganta da sauran abubuwa da ba zasu lissafu ba  duk a cikin shekara Daya.

Injiniya Sunusi Aminu Yero yayi kira ga alummar jihar Kaduna dasu tabbatar sun ci gaba da baiwa mai girma Gwamna goyon baya domin ci gaban Jihar  Kaduna  ya Kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC dasu hada kansu wuri daya domin zama tsintsiya madaurinki daya, wannan shi zaisa a kara samun ci gaba a cikin jam’ iyyarsa.

Leave a comment