AMNESTY INTERNATIONAL: Yadda Ake Yiwa Mata Fyade A Gidajen Yarin Maiduguri

Kungiyar kare hakin dan adam ta Amnesty International ta bayyana cewa ana yiwa mata da yara fyade a gidajen yarin gwamnati guda biyu a Maiduguri, babban birnin Jihar Bornno.

A lokacinda yake yiwa manema labarai bayanin yadda aka samu rahoton, mai magana da yawun kungiyar Amnesty International, Isa Sanusi ya ce sun dauki lokaci suna bincike akan jan hanakali da wani fursuna mai sauna Charles Okah yayi,inda ya ce an hada mata da yara da manyan maza a wuri daya, ana kuma cin zarafin matan da yaran ta hanyar yi masu fyade,ya ce wannan abin tashin hankali ne ganin cewa galibin fursunonin wadanda ta’addancin Boko haram ya daidaita su ne.

Sai dai hukumar kula da gidajen yarina kasa ta musanta zargin na kungiyar Amnesty.

Isa Sanusi, yayi kira ga gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Kula da Gidajen yari Francis Enobore ya ce wanan zargi ne Kungiyar Amnesty ta yi domin bai zo daidai da binciken da suka yi ba, duk da cewa suna cigaba da bin gidajen yarin kasar suna bincike.

Enobore ya ce gidajen yari da ke Maiduguri na cikin wadanda suke dubawa.

Leave a comment