Amfanin Shan Tea Ga Dan Adam

Bincike ya tabbatar da cewar Sinawa su suka kirkiro shan shayi (Tea) kuma sarkin kasar Sin Sheng Nong shi ne ya fara shan shayi a matsayin wani abin sha tun shekaru 2,737 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S). Wannan shi ya sa Sinawa ke da shayi iri-iri a matsayin magunguna.
Yayin da kuma shayin da ya zama ruwan-dare a Duniya wato Lipton wani mai suna Thomas Lipton dan kasar Scotland ne wanda aka haife shi a 1850 ya kirkiro wannan brand din kuma har yau ake amfani da sunansa Lipton. A shekarar 1889 ne Mista Lipton ya soma sayar da wannan shayi bayan da ya je kasar Ceylon wato wadda ake kira Srilanka a yanzu inda ya soma noman ganyen tea dinsa. Sai a shekarar 1906 Mista Lipton ya soma fitar da shayin Lipton zuwa kasar Japan.
To menene amfanin shan ganyen shayin Lipton ga lafiyar jama’a?
Masana kuma masu bincike kan ganyen shayin sun tabbatar da cewa yawan shan ganyen shayin Lipton na taimakawa kamar haka.
1 Shan Lipton kofi daya a kullun na rage saurin kamuwa da cutar sankara wato cancer.
2 Shan kofin Lipton daya da safe na kara inganci da kare lafiyar zuciya da hanyoyin jinni saboda yana dauke da wani sinadari da ake kira (Epigallocatechin gallate) da kuma sauran sinadari da ke hana toshewar hanyoyin jini.
3 Lipton tea na dauke da sinadarin Flabonoids da ke taimakawa jiki samun kuzari.
4 Yawan shan Lipton na kawar da kwayoyin cuta na baki don haka na maganin cututtukan baki da warin baki.
5 Yana taimakawa wajen narkar da kitse a jikin mutum don haka yana rage kiba da nauyin jiki sosai in aka jure shansa. Idan ana sha duk safiya da zarar an tashi a gado ba tare da an sanya masa suga ko wani abin zaki ba yana haifar da sakamako mai kyau na rage kiba.
6 Yana rage ciwon jiki da na gabobi domin Lipton tea na dauke da sinadaran EGCG wato Ephigalloncatechin gallate.
7 Yawan shan ganyen tea na Lipton yana sa kullun mutum ya zama kamar saurayi ko budurwa domin yana gyara lafiya da ingancin fatar jiki. Mai yawan shan Lipton tea kullun fatarsa za ta dinga laushi.
8 Yana rage yawan kitse a cikin jijiyoyin jini (Cholesterol) idan aka juri shansa a kullun.
9 Shan Lipton tea a kai a kai na rage yuwar kamuwa da ciwon suga musamman ma diabetes, domin yana kunshe da sinadaran da ke rage karuwa sugar a cikin jini.
10 Yana rage wasu kananun kumburi a jikin mutum domin yana kunshe da abin da ake kira Antiodidant.
11 Yawan shan Lipton kan kwantar da hankali kuma ya kawo natsuwa ga wanda ke cikin wani halin tashin hankali.
12 Shan Lipton tea na kara inganta garkuwar jiki saboda yana dauke da Bitamin C mai yawa. Domin haka yana rage saurin kamuwa da cututtuka masamman cutar mura.
13 Bincike ya tabbatar da cewar shan Lipton tea na rage yiyuwar kamuwa da Prostate Cancer. Sannan kuma bincike ya tabbatar da cewar matan da ke yawan shan Lipton tea sun fi matan da ba su shansa rashin kamuwa da sankarar nono/mama.
14 Yana rage yiyuwar kamuwa da Stroke wato katsewar bugun zuciya nan take. Domin yana kunshe da sinadarin da ke hana kaurin jijiyoyin jini.
15 Shan Lipton a-kai-a-kai na maganin mantuwa kuma na sanya ka ji garau a lokuta da dama. Dattijai da ke yawan shan Lipton tea sun fi wadanda ba su sha kaifin basira da rashin mantuwa kuma yana hana yuwar kamuwa da cutar Alzheimer.
16 Shan Lipton tea na maganin hawan jinni domin yana kunshe da sinadaran da ke daidaita karfin gudun jini a jiki.
17 A cikin Lipton tea akwai sinadarin Iron wanda ke maganin karancin jinni a jiki, domin haka yana taimakawa wajen cutar Anemia wato karancin jini a jiki.
19 Shan Lipton yana kare lafiyar koda da hanta sosai domin yana fitar da cututtuka daga koda da hanta kuma ya inganta ayyukansu ta yadda ba za su iya rike cututtuka ba.
20 Shan Lipton na rage karfin tari. Idan aka sha Lipton da ruwan zafi aka sa zuma yana amfani sosai. Kuma yana maganin ciwo ko zafin wuya. Ana shan Lipton ne da Lemongrass da ruwan dumi.
Matsalolin Da Shan Lipton Kan kawo
1 Hana barci cikin dare saboda caffeine da ke cikinsa. Amma bai kai na sauran tea yawa ba.
2 Masu ciwon koda, saboda shan Lipton tea na sanya yawan fitsari, zai fi kyau ku tuntubi likita. Lokacin shan Lipton da ya fi dacewa shi ne da sassafe sai kuma awa daya bayan cin abinci.

Leave a comment