An Kaddamar Da Littafinnan Mai suna “Past Question For Medical Laboratory Technician” A Zariya

Daga Idris Umar Zariya

A cikin satin daya gabatane aka kaddamar da littafin Saleh Ahmed mai suna PAST QUETION FOR MEDICAL LABORATORY TECHNICIAN tate da hadin guiwar majalisar matasa na karamar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna karkashin jagorancin komret Jibirin Salihi shugaban majalisar a karamar hukumar ta Sabin Gari an gudanar da taronne a bubban dakin taro na NITT zariya

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka halaci taron.

Taron ya samu karbuwa ta bangare daban daban musamman bangaren hukumomin ilmi da sarakuna.
Mawallafin mai suna Ahmed Saleh ya sami yabo a gurin Mayan baki kamar shugaban jami’ar Ahamadu bello Zariya farfesa Kabir Bala da wakilan hukumomin ilmi da suka halacci taron.

Manyan bakin sun jinjinawa marubucin tare da jinjina ga ingancin littafin a duniyar kimiyar gwajegwace na zamani

Hakan yasa da yawa daga cikin manyan bakin sukayi kira da gwamnati da ta tallafawa irinsu Ahmed Saleh don ci gaban ilmi a kasa bakin daya.

Hakan yasa mutane ke tambayar wanene Saleh Ahmed wanda ya wallafa littafin da aka kaddamar a wannan rana?

To shi dai Saleh Ahmed An haifi AHMAD SALEHI kuma ya girmane duk a garin Zariya, da ke jihar Kaduna. Ya yi makarantar Railway Staff School inda ya samu shaidar kammala makarantar firamare, daga nan kuma sai ya tafi sananniyar makarantar sakandiren nan wato kwalejin Barewa da ke Zariya inda ya samu shaidar kammala makarantar sakandire. Ya cigaba da karatu inda ya karanta fannin Medical Laboratory Technician (MLT) a makarantar School of Medical Laboratory Sciences da ke kwalejin Health Science and Technology, Tsafe a jihar Zamfara inda ya samu rijista Medical Laboratory Science Council of Nigeria (MLSCN) a matsayin mai rijistar MLT. A yanzu haka ya kammala karatun digiri dinsa a fannin Medical Laboratory Science daga jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).

Yana da kwarewa a fannin koyarwa da kuma aikin Medical Laboratory Technology na shekaru. A yanzu haka shine shugaban sashen Medical Laboratory Science a KASS College of Health Science and Technology da ke Dandume kuma malami mai ziyara domin koyarwa a Elite College of Health Science and Technology da ke Zariya.
Ahmed Saleh ya kasance mai fafutukar a bangaren lafiya kuma inda ya ke gabatar da jawabai a kafofin sadarwa.

A matsayinsa na mai aiki a matsayin mai ilimin kimiyyar Medical Laboratory, yana aiki tare da kara samun horo a kungiyoyin gwamnati da kuma wadanda ba na gwamnati ba. Ya yi aiki tare da El-Barau Medical and Diagnostic Centre, Zariya (2014 – 2017) ya ma kuma yi aiki domin taimakawa ga ma’aikatar lafiya ta jihar Kaduna domin yakar annobar Covid-19 a cikin shekarar 2020. A lokacin da ya ke a makaranta a matsayinsa na dalubi, ya ruke mukaman siyasa daban-daban wadanda suka hada da shugaban MELSA CHST Tsafe (2013 – 2014), Academic Director NIMELSS BUK (2018 – 2019), shugaban NIMELSS BUK (2019 – 2020), ciyaman na Academic Committee AMHS BUK (2019 – 2020) kuma ciyaman na PEC NIMELSSA na kasa (2019 – 2020) wadannan kadan kenan.

Ahmad Saleh ya kasance yana gabatar da jawabai ga kasa baki daya kuma ya samu lambobin yabo da dama a wuraren da akan gabatar da irin wadannan jawabai.

Abubuwan da su ke burgeshi sun hada da karatu, rubutu, tafiye-tafiye da kuma yin sabgogin abokai.

An kaddamar da littafin lafiya an tashi lafiya.

Leave a comment