Bayan Ya Datse Azzakarin Shi, Bobrisky Ya Sauya Halittarsa Zuwa Mace

Fitaccen mai mu’amala da yanar zigo a Nijeriya Idris Olarenwaju, wanda aka fi sani da suna Bobrisky, ya bayyana cewa lokaci yayi da Zai canza kamanninsa zuwa Ta Mata wanda hakan ya Sanya Shi Datse Azzakarin shi.

Bobrisky, ya bayyana haka ne a ranar Laraba a shafinsa na Instagram, inda ya wallafa wasu hotunanshi sanye da Kayan Mata wanda yace yanzu ya tabbatar da ya mayar da kanshi mace.
Ya Kara tabbatar da cewa baiyi nadamar Datse Azzakarin Shi ba ko kadan.

A ranar Talatar wannan makon Bobrisky ya bayyanawa duniya cewa ya Datse Azzakarin Shi domin baya kaunar ganinshi a jikinshi.

Leave a comment