TSARO : Rundunar ‘Yan Sanda Ta Haramta Ayyukan ‘Yan Kato Da Gora A Jihar Kaduna

Rundunar ‘Yan Sanda Ta jihar Kaduna ta sanar da haramta ayyukan kungiyoyin matasa ‘yan sa kai, wadanda aka fi sani da ‘YAN KATO DA GORA, a fadin jihar baki daya.

Rundunar ta sanar da haramta ayyukan kungiyoyin ne ta bakin kakakinta, DSP Yakubu Sabo cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba nan a jihar.

DSP Sabo ya bayyana cewa rundunar ‘Yan sanda tana gargadi kada wani ya sake bayyana kansa a matsayin dan kato da gora, balle kuma ya aikata wani aiki da sunan tsaro a gaba daya jihar Kaduna.

Ya Kara da cewa duk wanda hukumar ‘Yan sanda ta kama ya karya wannan umarni zai gamu da fushin hukuma, kuma za’a yi amfani da duk hanyoyin da doka ta tanadar don hukuntashi, ko wanene.

Akan haka rundunar ‘Yan sandan ya bukaci Goyon baya da hadin kai ga jama’a ta wajen bata muhimman bayanai game da ayyukan miyagu a unguwanninsu domin rundunar ta samu daman karesu yadda ya kamata.” Inji shi.

Leave a comment