Ko Kun San Itacen Dalbejiya Na Maganin Sanko?

Kamar yadda aka sani ne Itacen dalbejiya ko kuma dogon yaro da turanci kuma ‘Neem tree’ itace ce da ke da daci amma tana da matukar amfani ga mutum.
Da shi a sha ruwan, yin amfani da man sa da kuma ganyen sa na maganin gaske a jikin mutum, kamar yadda Katsina Post ta samo daga shafin j
Ga wasu hanyoyi da amfani da dalbejiya ke yi a jikin mutum:
1. Ganyan dalbejiya na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya musamman idan aka dafa ganyen ana shan ruwan kamar shayi.
2. Ganyen dalbejiya na taimakawa wajen tacewa da tsaftace jinin mutum a jikin sa.
3. Ganyen na maganin cutar zazzabin cizon sauro da Typhoid.
4. Yana kuma maganin cutar ciwon ciki musamman idan cikin mutum ya murde saboda wani abincin da aka ci.
5. Ganyen dalbejiya da man shi na gyara fatar jikin mutum.
6. Ganyen na maganin saiko, magance amosanin kai da kuma sa tawon gashi a kai.
7. Ana iya amfani da man dalbejiya a matsayin dabarar bada tazarar iyali.
8. Ganyen na kawar da cutar daji musamman dajin dake kama nono, ‘ya’yan maraina sannan yawan amfani da ita na hana kamuwa da cutar.
9. Ganyen na maganin cutar gyambon ciki wato ‘Ulcer’ da kuma rauni a jiki.
10. Yana rage kiba a jiki musamman ga masu fama da ita.
11. Yana warkar da ciwon gabobi da ciwon kai.
12. Yana kare mutum daga kamuwa da cutukan da ake samu ta hanyar yin juma’i
13. Warkar da kuturta.
14. Yana maganin ciwon ido.
15. Yana maganin guba da ake samu daga jikin dabba kamar cizon cinnaka, maciji da sauransu.
16. Ganyen na maganin kwari musamman wadanda ke lalata amfanin gona.

Leave a comment