Gwamnatin Kano Zata Hukunta Masu Kin Tsaftace Muhallinsu

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa zata dauki matakai masu tsauri akan duk wanda ta sake kamawa da bujirewa na kin tsaftace muhallansu ko harabar sana’arsu.
Babban Sakataren ma’aikatar muhalli na jihar Kano Alhaji Ibrahim Halilu Dan-Tiye ne ya bayyana hakan yayin ran-gadin duba tsaftar muhalli na karshen wata.
Dan-Tiye yace, a zagayen da tawagar ta yi , masu ababen-hawa da dama da dai-daikun mutane sun fito suna ta hada-hada su a maimakon tsaftace muhalli.
Wasu daga cikin mutane da aka ci su tara sun bayyana nadamarsu tare da neman afuwar Gwamnati.
Babban Sakataren ya kuma ja hankalin al’umma da su kasance masu bin doka da oda don kaucewa hukunci

Leave a comment