KADUNA: Dan Majalisa Ya Raba Wa Al’ummar Mazabarsa Goron Sallah


Daga SHEHU YAHAYA, Kaduna

Dan majalisar Dokikin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar gungumar  Kawo a majalisar Dokikin Jihar Kaduna, Honarabul Nazir Sanusi Abubakar , ya raba wa al’ummar mazabarsa tallafin kudi da ragunan layya domin gudanar da bikin sallah.


Dan Majalisar ya yi rabon kudin ne rukuni-rukuni, inda wadansu mazabun suka samu naira Dubu Dari biyu da raguna  yayin da wasu manyan ‘yan siyasa suka samu tallafin kudi  da raguna.

A ziyarar da ‘yan jaridu suka kai a cikin mazabu Biyan na Dan majalisar sun zanta da wadanda suka amfana da tallafin inda suka Yaba da kokarin Dan majalisar a dai dai lolacin da ake cikin halin kunci da talauci.


Binciken wakilinmu ya nuna cewa  mazabar Badarawa/Malali sun samu tallafin naira dubu dari biyu baya ga wasu dai-daikun ‘yan siyasa da Dan majalisar yayi musu Tallafi na musamman.

Haka Suma mazabar Unguwar Dosa Suma sun samu irin wannan Tallafi.

Umar Samfam, jigo ne a jam’iyyar APC a Mazabar Badarawa Malali yace” Mun raba naira Dubu Dari biyu Wanda tuni muka rabawa mutane domin gudanar da shagul-gulan sallah”

“Mun godewa Honorabul Naziru bisa wannan kokarin Wanda a watan Azumi ma yayi irin wannan tallafin. Kuma fa akwai wasu wadanda suka samu raguna da kudi akalla Dubu 50-50, saboda haka Muna godiya da wannan kokarin”



Yusuf Umar, mazaunin mazabar Unguwar Dosa ne yace ”  Alhamdulillahi, Muna godiya ga Honorabul Naziru Sanusi Abubakar, Yana kasa mai tsarki Yana ibada tun daga can ya zuro hannunsa mai tsarki ya turo mana goron Sallah yace muyi Sallah cikin murna da farin ciki saboda haka Muna kira ga sauran ‘yan siyasa da sayi koyi da irin halin Dan majalisar mu na Kawo wajen tallawa Al’ummar mazabarsa ” inji shi.

Leave a comment