Koyi Da Halin Marigayi Ali Akilu Zai Taimaka Wajen Samar  Shugabanci Na Gari  A Arewa- Dakta Ibrahim Gusau

Dakta Ibrahim Aminu Gusau

Tsohon Dakarta a hukumar Yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa EFCC Dakta Aminu Ibrahim Gusau, ya bayyana cewa koyi da rayuwar marigayi Ali Akilu zai Taimaka  wajen samar da shugabanci na gari a Arewacin Kasar nan baki daya. Dakta Ibrahim Gusau, ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a Kaduna yayin kaddamar da littafi akan rayuwar marigayi Ali Akilu.

” Koyi da rayuwar marigayi Ali Akilu shine kedai mafita akan gyara yanayin shugabanci a Arewa saboda sun bar abubuwan  koyi  na gari Wanda yanzu sune  muke tunkaho da su.  Wannan taro tuni ya kamata ayi shi Amma  yanzu ma lokaci Bai kure ba saboda haka Muna fatan zamuyi amfani da abubuwa daga halayyan da su marigayi Ali Akilu ba Wai kawai mu azo a zauna jin lacca ba Wanda zai zama kamar taron shan shayi kawai “

Dakta Gusau, ya nuna damuwarsa akan halin rashin taron da Arewa take ciki Inda yace lamari ne da ya jefa yankin cikin mawuyacin halin koma baya a bangaren haekokin noma da tattalin arzikin yankin.

Ya bukaci gwqmnatocin yankin da suka zage damtse wajen ceto yankin daga cikin natsalar da al’umma suke ciki.

Leave a comment