Hukumar Kwastam Ta Kama Wasu Makamai A Legas

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya ta kama wasu makamai masu yawa da aka yi kokarin shigar da su Najeriya06e1031f-c0c0-4d5b-aaca-f0255b24edff_cx0_cy4_cw0_w987_r1_s_r1

Hukumar ta bayyana cewa ta kama wasu akwatuna dauke da bindigogi 661 a cikin wasu akwatuna 49 da ake tafiya da su a wata mota a yankin Apapa dake Legas.

Kakakin hukumar Kwastan mai kula da shiya ta shida Mista Jerry Attah, ya fadawa Muryar Amurka cewa yanzu haka an kama wasu jami’an hukumar biyu da kuma wasu fararen hula biyu.

Sai dai har yanzu ba a bayyana sunayen mutanen da ake zargi da yanzu haka ke hannun hukuma ba. wannan lamari dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumomin tsaro ke kokarin dakile ayyukan ta’addanci da maido da zaman lafiya a Najeriya.

Leave a comment