Gwamnatin Tarayya Zata Ciyar Da Dalibai Miliyan Daya Abinci A Wannan Makon

​Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata fara ciyar da daliban makaranta sama da miliyan daya abinci a wannan mako wanda tuni ta dauki masu dafa abinci guda 11,775 domin fara girkin.

Mai taimakawa mataimakin shugaban kasa , Yemi Osinbajo, NA kafafen yada labarai  Laolu Akande shi ya sanar da haka ga manema labarai.

Akande, yace jimillan kudi naira 844, 360, 550 gwamnatin tarayya ta baiwa  jihohin Anambra, Ebonyi, Enugu, Oyo, Osun, Ogun da Zamfara a karshen mako.

Yace gwamnatin tarayya ta ware makudan kudade domin ciyar da daliban makarantar firamare miliyan daya a jihohi bakwai.

Yace a jihohin  Anambra, Enugu, Osun, Ogun, da Oyo tuni aka fara ciyarwan inda yace a wannan makon  za a fara ciyarwan a jihohin Ebonyi da Zamfara, Wanda dama an basu kudinsu.

Yace gwamnatin Buhari zata ciyar da dalibai miliyan 1, 043, 205 a jihohi bakwai a wannan makon.

Jimillan masu girka abinci guda 11,775 aka dauka haka kuna kananan manoma an basu aikin noma abincin da za a dafawa dalibai.

Jihar Anambra,  itace ta farko da aka fara aiwatar da ciyarwa na gwamnatin tarayya a shekarar data gabata wanda ake ciyar da makarantu guda 30 a kullum akan kudi naira miliyan 188, 769,000, wanda masu girki guda  937 zasu dafawa dalibai  96,489 abinci.

Jihar Ebonyi, gwamnatin tarayya naira miliyan 115, 218, 600, Wanda an dauki masu girki guda  1466 domin ciyar da dalibai guda 164, 598.

Gwamnatin tarayya ta ba jihar Enugu naira miliyan 67,244, 800  domin ciyar da dalibai guda  96, 064  kana an dauki masu dafa abinci guda1128.

Itama jihar Ogun gwamnatin tarayya ta basu kudi naira miliyan 119, 648, 900 domin ciyar da dalibai guda  170, 927 Wanda kuma an dauki masu girki guda  1,381.

Sai jihar Osun, an basu kudi naira miliyan 92, 425, 400 domin ciyar da dalibai guda  142, 193 Wanda aka dauki masu girki guda 2,688.

A jihar Oyo gwamnatin tarayya ta bada kudi naira miliyan 72, 288, 300 domin ciyar da dalibai guda  103, 269 haka kuma an dauka masu girki guda 1437.

A jihar  Zamfara gwamnatin tarayya ta bayar da kudi naira miliyan 188, 765, 500  domin ciyar da dalibai guda 269, 665 wanda kuma an dauki masu girki guda 2, 720

Leave a comment