‘Yan Majalisar Jihar Kaduna Na Yunkurin Tsige Gwamna El-Rufa’i


Rahotanni daga zaure majalisar dokokin jihar Kaduna sun bayyana tabbatar da cewa  wasu ‘yan majalisar jihar sun fara yunkurin tsige gwamnan jihar malam Nasiru  Ahmed El-Rufa’i, bisa abin da suka ce gwamnan yana mulkin kama karya.

‘Yan majaliasar wadanda  sun kai su 14 da suka yanke shawarar tsige gwamnan. A wani taro da suka yi a gidan daya daga cikin ‘yan majaliasar inda suka ce zunuban gwamnan sun cancanci a tsige shi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa shirin tsige gwamna ya samo tushe ne daga magoya bayan sanata suleman Hukunyi ne a majalisar wanda dan majalisa daga karamar hukumar Giwa yake jagoranta, wadanda yanzu haka suke kara samun goyon baya daga sauran ‘yan majalisun. Ya zuwa lokacin da muke rubuta wannan rahoto akwai ‘yan majalisu guda 7 daga kudancin kaduna sai guda 7 daga Arewacin jihar wadanda duk suna goyon bayan tsige gwamnan.

Daga cikin zunuban da ‘yan majalisar sukace  gwamnan ya aikata sun hada da: rashin yiwa shugaba Buhari biyayya lokacin rashin lafiyarsa ta hanyar neman kujerar mataimakin shugaban kasa da kuma rashin halartar tarukan addu’oin samun sauki ga Buhari Wanda aka gudanar a jihar da wasu sassa daban daban.

Hakazalika, sunce gwamna El-Rufa’i, ya karkatar da dala miliyan 100 na jihar domin farfado da kamfanin kaninsa na INTERCELLULAR,  da kuma karkatar da wasu kudi naira biliyan 30 wanda shugaban kasa ba bayar domin biyan ma’aikata da  kuma karbo bashi daga hukumar  bayar da bashi na kasa da kasa wato PARIS CLUB.

Sauran laifukan sun hada da rashin biyayya ga sarakuna da shugabannin addinai da kuma yin sakaci akan rikicin kudancin jihar kaduna. Hakazalika, sun ce gwamnan yana azabtar da malaman makaranta na rashin biyansu albashinsu.

‘Yan majalisun, sun bayyana cewa tuni gwamnan ya fara yunkurin sayar da wasu kaddarorin jihar da suke jihar Legas Da Abuja ga abokanshi wanda hakan suka ce mulkin kama karya ne wanda bazasu amince da hakan ba.

Rohotanni, sun ruwaito cewa ruwa ya fara tsami tsakanin sanata Hukunyi da Gwamnan wanda shi Hukunyi ya  zama daraktan yakin neman zaben gwamnan a zaben 2015 da ya gabata, wanda hakan ya sanya magoya bayan Hunkuyi a majaliasar suka fara yunkurin tsige gwannan.

Leave a comment