Jam’iyyar APC ta jihar Kaduna ta koka dangane da yadda talauci yayi mata katutu wanda hakan yana haifar musu da matsaloli wajen tafiyar da aikinsu a jihar
Bayanin haka ya fito ne daga bakin sakataran jam’iyyar Yahaya Baba Pate, yayin da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron shugabannin jam’iyyar wanda ya gudana a jiya.
Baba Pate, ya bayyana cewa jam’iyyar bata samun tallafi daga wurin ‘ya’yan jam’iyyar masu rike da madafun iko inda yace suna ji a jikinsu na rashin kudi.
Ya bayyana cewa masu rike da mukamai daga karamar Hukumar zariya sune kadai suke Tallafawa jam’iyyar, a cewarsa, sauran basa tabuka komai
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar su ta samu nasarori da dama a cikin shekara daya.