Rikicin APC: Shehu Sani Da Tijjani Ramalan Sun Kauracewa Taron APC A Kaduna

Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta bayyana goyon bayanta ga gwamnan jihar malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, bisa aiwatar da ayyukan ci gaban jihar baki daya.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne Jim kadan bayan kammala taron jiga-jigar jam’iyyar a jihar.

Hajiya Binta Mu’azu, itace ta bayyana hakan a madadin sauran shugabannin jam’iyyar, inda tace sun gamsu da gwamnatin El-Rufa’i bisa ganin yadda yake kawo abubuwan ci gaban jihar.

Sai dai kuma shugaban kwamitin jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Alhaji Tijjani Ramalan, da Sanata Shehu Sani da Isa Ashiru da kuma Alhaji Haruna Sa’eed Kajuru, duk basu halarci taron ba, hasalima, ba’a fadi dalilansu na rashin halarta  taron ba lamarin da ke kara nuna cewa har yanzu akwai matsala a kwance a jam’iyyar APC a jihar Kaduna .

Taron na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na jihar Kaduna ya samu halarcin gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru El-Rufa’i da mataimakinsa da sakataran gwamnatin jihar da kuma kakakin majalisar dokokin jihar. Sauran sun hada da  Sanata Suleiman Hunkinyi da wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilai da na dokokin jihar.
Tijjani Ramalan, Wanda shine yayi ta kokawa dangane da rashin gudanar da taron  masu ruwa da tsakin jam’iyyar, Wanda hakan ya sanya aka shirya taron amma bai halarci taron ba.r a wurintaron

A jawabin sa sakataran jam’iyyar na jiha Alhaji Yahaya Baba Pate, ya zayyano irin nasarorin da jam’iyyar ta samu cikin shekara daya inda yace sun samu nasarar hada  kan ‘ya’yan jam’iyyar a kananan hukumomi jihar.

Sai dai sakataran jam’iyyar ya koka dangane da yadda jam’iyyar take fama da talauci da rashin samun tallafi daga wurin masu rike da madafun iko a jihar. 

A dadai lokacin da ake gudanar da taron, wani bangare na jam’iyyar bisa jagorancin mataimaki Tom maiyashi suma sun gunadar da masu taron a wani muhalli daban.

Leave a comment