Zamu Tabbatar Da Mun Tallafawa Gwamna  El-Rufa’i ….Hon. Bello Gimi

Shugaban kwamitin Kudi na majalisar dokokin jihar Kaduna Hon. Bello Sani Gimi, ya bayar da tabbacin cewa zasu ci gaba da tallafawa gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i wajen ganin an kara inganta hanyoyin samun kudadan Shiga domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban jihar baki daya.

Bello Gimi, Wanda kuma shine Dan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar mazabar karamar hukumar Makarfi ya kuma bayyana cewa ya zuwa yanzu al’ummar jihar suke sun gamsu da yadda gwamnatin ta fara aiwatar da ayyukan raya jihar lungu da sako a fadin jihar Wanda hakan, a cewarsa, alamace da ke nuna gwamnatin ta himmatu wajen kashe kudin ta hanyar da ya kamata.

Dan majalisar ya bayyana haka ne a jawabinsa Jim kadan bayan wata kungiyar yan jarida ta bashi lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen ciyar da jihar Kaduna gaba da kuma mazabarsa.

Akan hakan Dan majalisar yayi alkawarin ci gaba da kawo abubuwan ci gaban mazabarsa da kuma jihar Kaduna baki daya inda yace a matsayinsa na Dan majalisa zai iya bakin kokarinsa wajen ganin ya kawo kudirorin da zasu kawo ci gaban jihar Kaduna.

Leave a comment