Gwamnatin Kaduna Zata Fara Bada Katin Shaidar  Zama Dan Jihar


Gwamnatin jihar Kaduna  ta kammala duk shirye-shiryenta na fara yiwa daukacin al’ummar jihar rijistan zama Dan asalin jihar ta hanyar basu katin shaidar zama Dan jihar Kaduna.

Aikin bada katin shaidan za’a fara shi a ranar talata  mai zuwa  wato ranar 2 ga watan mayu a sakatariyar kananan hukumomin jihar 23, inda gwamnatin  tace rijistan zai bawa gwamnatin Samar  sanin ainihin yawan al’ummar jihar da kuma sanin yawan ma’aikatan jihar, hasalima, gwamnatin zata san ainihin ‘yan asalin jihar Kaduna.

A wata sanarwa da gwamnatin take yayatawa a kafafan yada labaran jihar, tace akwai matsala  ga  duk wani mutum da baiyi rijistan ba, akan hakan tana bukutar al’ummar jihar da su gaggauta yin rijistar da zarar an fara rijistar.

Wannan sanarwa ta gwamnati ya fara haifar da CeCe Ku ce a tsakanin al’ummar jihar, inda  da dama jama’ar jihar suke Allah wadai da wannan mataki na gwamnatin jihar.

Gwamnatin tace zata hada hannu da hukumar bada katin shaidar Dan kasa ta gwamnatin tarayya Wanda duk Wanda za’a yiwa rijistar sai ya nuna katin shaidar Dan kasa kamin ayi masa zaben.

Leave a comment