Zamu Kawo Zaman Lafiya A IPMAN                  … Inji  Hon. Abdulfatah 

Shugaban kwamitin riko na kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) na kasa shiyyar Kaduna Hon. Abdulfatah Murtala, ya bayyana cewa zasu yi bakin kokarinsu na ganin sun kawo Zaman Lafiya a cikin kungiyar inda yace burinsu shine a samu Zaman Lafiya da hadin kan daukacin ya’yan kungiyar.

Hon. Abdulfatah, yace uwar kungiyar su ta (IPMAN) ta kasa itace ta kafa kwamtinsu domin ganin an kawo Zaman Lafiya a cikin kungiyar, yana mai shawartar ‘ya’yan kungiyar da su basu goyon baya domin tabbatar da  Zaman Lafiya a kungiyar.

Shugaban ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai, inda yace baya ga kwamitin riko da aka kafa, an kuma kafa kwamitin dattawa wadanda zasu tabbatar da sun kara hada ‘ya’yan kungiyar. Yace an dauko dattawa masu fadi aji a harkar man fetur kuma masu kuma, saboda, a cewarsa lokaci yayi da za’a samu Zaman Lafiya a kungiyar IPMAN a Kaduna.

Hon. Abdulfatah Wanda kuma shine Shugaban kamfanin hada- hadar man fetur na ( Yusuffa) ya kara da cewa yanzu haka sun kai takardar kama aikinsu ba kwamishinan ‘yan sandar jihar Kaduna da fadat gwamnatin jihar da mahukuntar matatar man fetur ta Kaduna da daukacin jami’an tsaron jihar Kaduna.

Akan haka, ya bukaci daukacin ya’yan kungiyar da ci gaba da basu goyon bayan da suka kamata domin ganin an samu Zaman Lafiya a cikin kungiyar IPMAN.

Idan za’a iya tunawa Kungiyar IPMAN ta sha fama da rikicin shugabanci lamarin da ya hana gudanar da zabe amma yanzu ‘ya’yan kungiyar suna ganin za’a samu Zaman Lafiya bisa kafa kwamitin.

Leave a comment