Zasu  Gina Matatar Man Fetur A Jihar Kaduna

A kokarin ganin an kara bunkasa ci gaban  tattalin arzikin jihar Kaduna, gwamnatin jihar da wani kamfani a kasar Sin wato (China) zasu Gina matatar man fetur wacce zata rinka tace  danyan man  fetur ganga Dubu 50 a kowacce rana.

Gwamnatin da kamfanin na kasar China mai suna ( China  Machinery Engineering Corporation)  sun rattaba hannu a wata takardar  yarjejeniya  da fahimtar juna akan Gina matatar man fetur a jihar ta kaduna.

Da yake sanya hannu a madadin gwamnatin jihar Kaduna a kasar ta China , gwamna Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewa Gina matatar man zata taimaka wajen kawo bunkasar tattalin arzikin jihar Kaduna baki daya, inda kamfanin na kasar China shine zai Gina matatar man da kuma shimfida bututun man fetur daga bakin iyakar kasar Jamhuriyar Nijar da Kaduna mai tsawon Nisan kilomita 400 Wanda daga nan ne  za’a rinka turo danyan man fetur.

Haka kuma domin ganin matatar man tayi aiki yadda  ya kamata, za’a Samar da cibiyar Samar da wutar lantarki mai Zaman kanta wacce zata Samar da wutan lantarki mai karfin 80-100 MW ga matatar Wanda kuma zai kasance a kusa da matatar.

Gwamnatin jihar Kaduna da kamfanin na CMEC duk sun amince zasuyi aiki tare domin ganin sun cika alkawarin da suka daukarwa juna.

Hakazalika, gwamnatin ta Sanya hannu a kan yarjejeniyar inganta harkar sugurin jiragen sama, Wanda nan ma kamfanin sufurin jiragen sama na kasar China (COMA) zai inganta harkar jiragen sama  a filin tashi da saukar jirage na kaduna ta hanyar karbar jiragen  Medview da Chanchangi haya.

Leave a comment