A kokarinta na bunkasa harkar ilimi da lafiya a jihar kaduna, gwamnatin jihar ta bayyana cewa zata tura dalibai Mata guda 300 Karatun Likita a Kasar Cuba domin samo ilimin Likita.
Gwamnatin tace za’a Fara tura daliban Kasar Cuba ne daga farkon zangon karatu na shekara 2018/ 2019 wanda Kuma Gwamnatin ta kammala duk wani shirin da Suka kamata Akan tafiyar daliban.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin gwamnan jihar kaduna Nasiru Ahmed El-rufai, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na TWITTER inda yace a duk shekara Gwamnatin zata rinka tura dalibai Mata 300 zuwa Kasar Cuba domin Karatun Likita, a cewarsa hakan Zai Kara sanyawa a samu yawaitar Mata likitoci a asibitocin jihar kaduna baki daya.
Hakazalika, gwamna El-rufai ya ce Gwamnatin jihar kaduna zata Gina magana’antar sarrafa magunguna a cikin jihar wanda ‘yan Kasar Cuba ne zasu hada hannu da gwamnatin wajen gina magana’antar.
A cewarsa, gwamnatin sa zata sayo magunguna daga Kasar Cuba masu yawa wadanda za’a raba a daukacin asibitocin jihar domin tabbatar da cewa ta cika alkawarin ta na inganta Harkar lafiya a fadin jihar baki daya.