ZAMFARA: An Halaka Makiyaya 15 A Harin Bawon Dajj

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar makiyaya goma sha biyar a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Muhammad Shehu, ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kai harin ne a kauyen Bawon-Daji da ke karamar hukumar Anka.
A cewar sa,shugaban karamar hukumar Anka Alhaji Mustapha Gado Anka ya shaida musu cewa, ‘yan bindigar sun je kauyen ne akan babura da misalin karfe 1:00pm, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani suka tsere zuwa cikin dajin da ke makwabtaka da kauyen.
Ko a baya-bayan nan ma ‘yan bindigar sun kai hari a jihar ta Zamfara inda suka kashe mutane da dama.

Leave a comment