Jami’ar Karatu daka gida ta ja hankalin dalibai da jami’an tsaro da sauran al’umma gaba daya kan takardun jarrabawar na bogi da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani da ke ake zargin daga hukumar makarantar suka fito.
Jami’in yada labaran Jami’ar ta NOUN Ibrahim Sheme ne ya bayyana haka a birnin tarayya Abuja.
Inda ya ce babu wata takardar jarrabawar da ta fito daga hukumar makarantar a hukuman ce ya kuma bukaci al’umma da su kaucewa batun.
Ya kuma ce jama’ar na iya kokarin ta wajen ganin ta girmama kanta da kare martabarta a idon duniya daga dukkanin irin wadannan abubuwan da ke faru da basu da tushe ballantana makama.
Sheme ya kara da cewa jami’ar ta NOUN ta shigar da korafi a rubuce ga hukumomin tsaro, inda ta bukaci jami’an tsaron su bankado wanda ke da hannu kan wajen yada bayanan domin gurfanar da shi a gaban kuliya.