An Dakatar Da Shugaban Karamar Hukumar Danbatta

Majalisar kansiloli ta karamar hukumar Dambatta da ke jihar Kano ta dakatar da mukaddashi kuma mai rikon kwaryar shugabancin karamar hukumar Alhaji Musa Sani Dambatta na

tsawon watanni shida.
Ajiya ne dai majalisar dokokin jihar Kano ta nada Alhaji Musa Sani Dambatta a matsayin shugaban riko na karamar hukumar biyo bayan dakatar da shugaban karamar hukumar Alhaji Idris Haruna Zago.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban majalisar kansilolin Hamisu Magaji Galadima.
Ta cikin sanarwar dai majalisar kansilolin ta kuma zargi mai rikon kwaryar shugabancin karamar hukumar da aikata laifuka guda hudu.
Laifukan da kansilolin suka zargi mukaddashin shugaban karamar hukumar da aikatawa sun hada da: Rashin girmama majalisar kansilolin da fitar da sirrin karamar hukumar da hadakai da wasu mutane domin ta da fitina a karamar hukumar da kuma kin bin tsarin mulkin kasa.
Majalisar kansilolin ta cikin sanarwar dai ta ce, ta mika da kwafin takardar ga majalisar dokokin jihar Kano da kwamishinan ‘yansanda na jihar Kano da kuma daraktan hukumar tsaron sirri ta DSS.
Sauran sune: Shugaban jam’iyyar APC da babban jami’in dansanda a karamar hukumar Dambatta da jami’in hukumar tsaron sirri ta DSS a karamar hukumar ta Dambatta da kuma hukumar kiyaye hadura ta kasa shiyyar Dambatta.
A wani labarin kuma a jiya ne shugabannin majalisun dokokin tarayya suka ce ziyarar da suka kai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Asorok tana alaka ne da katsalandan da sufeto Janar na ‘yansandan kasar Ibrahim Idris ke yi game da batun Dino Melaye da batun kasafin kudin bana da kuma ziyarar da shugaban kasar ya kai Amurka.

Leave a comment