Talauci Da Kuncin Rayuwa Sune Silar Rashin Zaman Lafiya A Nijeriya- Sheikh Arabi

Daga Shehu Yahaya

Shugaban Kungiyar Fityanul Islam ta kasa Sheikh  Muhammad Arabi Ahmad Abul -Fatahi, ya bayyana cewa Talauci da rashin aikinyi sune dalilan rashin tsaro da yayiwa  Arewacin Kasar nan katutu.

Sheikh Al’Arabi yace Al’umma Suna cikin mawuyacin haii na rashin tsaro da rayuwar kunci inda ya bayyana yunwa da talauci  sune silar sace -sace da muyagun ayyuka a Nijeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne jawabinsa yayi Bude taron majalisar koli kungiyar fityanu wanda aka gudanar a jihar Kaduna.

“Muna kira ga kungiyar gwamnonin Nijeriya da su tabbatar da cewa sun ceto rayuwar al’ummar su saboda ‘Yan  Nijeriya suna cikin kuncin rayuwa da rashin zaman lafiya”

Ya kara da cewa “Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta sauke nauyin da ta daukarwa al’ummar ta kamin zabe”

“Mafita shine a koma ga Allah Sai halayen al’umma su gyaru  ba zan manta a shekarun baya ba lokacin muna matasa Ba’a rufe gidajenmu da dare har abinci ake ajiyawa saboda baki, idan bako ya shigo ba Sai ya nemi abinci ba  Amma yanzu abin ba haka yake ba” 

Da yake bayani akan iftila’in tashin Bam na Tudun Biri , shugaban ya  bayyana gansuwarsu da irin matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka yayin faruwar lamarin na Bawa mutanan gudummawar gaggawa. 

Akan Hakan ya  bukaci gwamnatin tarayya Data tabbatar da  ta hukunta wadanda suka kai harin tare da cika alkawarin da  gwamnati ta  daukarwa al’ummar kasar  na kare rayuka da dukiyar al’ummar kasar baki daya.

Shugaban Taron Sanata Abu Ibrahim, yace ya zama wajibi al’umma su dage  da addu’a domin  samun zaman lafiya a Nijeriya. 

Yace Babu wata gwamnatin da zata goyi Bayan sace -sace da rashin zaman lafiya.

Abu Ibrahim, wanda Sanata Mukhtar  Mohammed  Dan Dutse ya wakilta, ya taya kungiyar  Fityanul Islam murnar cikar shekara 60 da kafuwa.

Ganin yadda kungiyar ta dade tana bayar da gudummawa wajen tallafawa addinin musulunci, akwai bukatar a samar da jami’ar musulunci mallakin Fityanul.

 Yayi alkawarin jagorantar ganin an samar da jami’an inda yace “zamu taimaka wajen yi mata rijista nan da shekaru hudu masu zuwa”

A nasa jawabin gwamnan jihar Kaduna, sanata Uba Sani, yayi alkawarin bayar da fili kyauta ga kungiyar fityanu domin gina jami’a ta musulunci mallakar kungiyar a jihar Kaduna.

” Nayi alkwarin ranar talata zan bada filin da za’a gina jami’an musulunci mallakin Fityanul Islam kuma ni zan jagoranci tabbatar da gina ta

Leave a comment