Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Haramtawa Sarakuna Bada Izinin Hakar Ma’adanai 

Daga Shehu Yahaya

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan dokar  haramta wa sarakunan gargajiya bayar da takardar amincewa don hakar ma’adanai a fadin jihar.

Mataimaki na musamman ga  gwamna Dauda, akan harkokin yada labarai  Sulaiman Bala Idris, ya bayyana haka a sanarwar manema labarai .

  A cewarsa, dokar  ta haramta duk wasu  neman izinin hakar ma’adanai. Inda yace  “Wannan ya haɗa da Neman izini da ga mutane, kamfanoni, ko ƙungiyoyi don hakar ma’adinai.”

Gwamna Lawal ya sake nanata cewa an yanke hukuncin ne saboda tsananin hatsarin da ke tattare da yawaitar fitar da takardun  amincewa na hakar Ma’adanan.

 “A yau, a matakin da gwamnatina ta dauka na magance matsalar rashin tsaro, na sanya hannu kan doka da ta haramta wa sarakunan gargajiya bayar da takardar amincewa  hakar ma’adanai a fadin kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.

“Kamar yadda babban mai shari’a ya bayyana, an gano ayyukan hakar ma’adanai a Zamfara a matsayin wani muhimmin al’amari da ke kawo tabarbarewar tsaro a jihar, musamman matsalar ‘yan fashin Daji”.

“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi mana jagoranci wajan  kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”

Leave a comment