Birnin Gwari Itace Tafi Kowacce Yanki Yawan Albarkatun Ma’adanai A Nijeriya-  Dr. Nura Hussaini 

Dr. Mohammed Nura Sani Hussaini

Daga Shehu Yahaya

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa a duk fadin Nijeriya  yankin Birnin Gwari mai fama da matsalar tsaro shine yankin da yafi  kowanne yanki yawan Albarkatun Ma’adanai sama da shekaru 100 da suka gabata.

Bayanin Hakan Ya fito ne daga Bakin Shugaban Kamfanin bunkasa Albarkatun Ma’adanai na jihar Kaduna Dakta  Mohammed Nura Sani Hussaini, a zantawarsa da wakilinmu,  inda yace tuni Gwamnatin jihar ta fara Nemo masu saka hannun Jari a bangaran domin bunqasa tattalin arzikin jihar baki daya.

Shugaban yace sama da shekaru 100 da suka gabata babu irin nau’in Ma’adanan da babu a Birnin Gwari, rashin tsaro ya Sanya an bar su kara zube wanda yanzu suke kokarin farfado dasu.

Yace  yanzu Gwamnatin jihar Kaduna ta dukufa wajen daukar matakan tsaro a yankin domin samun Daman hako Ma’adanan wanda zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma baki dada, a cewarsa , an fara samun sauqin kai hare-hare a yankin.

Shugaban ya kara da cewa tuni manyan kamfanonin hakar ma’adanai suka nuna sha’awarsu na shigowa yankin domin fara hakar ma’adanai wanda nan gaba kadan za’a Bude yankin domin fara aiki gadan-gadan.

Yace Har yanzu Gwamnatin jihar Kaduna Bata bayar da salilin hakar ma’adanai a Birnin Gwari ba Yana  Mai cewa duk wanda yake aiki a yankin to sojan gona ne.

Akan Hakan, ya nuna rashin Jin dadinsu dangane da yawaitar samun masu hakar ma’adanai a yankin ba bisa ka’ida ba, wanda suke taimakawa wajen gurbata tarbiyyar  matasan yankin.

Leave a comment