KADUNA: Gwamnatin Tarayya Tana Bin Masu Hakar Ma’adanai Bashin Naira  Biliyan 3.5 – Minista

Injiniya Kutama Hosea Ali

Daga Shehu Yahaya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana bin masu hakar ma’adanai a jihar Kaduna bashin naira biliyan uku da rabi ( 3.5) 

Bayanin Hakan ya fito ne daga bakin Ministan Harkokin Ma’adanai na tarayya  Cif Henry  Dele Alake, a wani taro da yayi da qungiyoyi masu hakar ma’adanai da dangonginsa a jihar Kaduna.

Ministry wanda  Shugaban Sashin Hakar ma’adanai  ba shiyyar Arewa Mason yamma na ma’aikatar  Injiniya  Kutama Hosea Ali, ya wakilta, ya jaddada cewa wajibi ne kungiyoyin masu hakar ma’adanai su biya kudin wanda suke zama a matsayin kudadan sabunta lasisin da aka basu na hakar ma’adanai. 

” Gwamnatin tarayya tana bin masu hakar ma’adanai bashing naira Tiriliyan 3 a fadin kasar nan wanda daga ciki tana bin masu hakar ma’adanai na jihar kaduna bashin Biliyan 3.5, wanda idan da sun biya kudin gwamnati zatayi amfani da su wajen aiwatar da ayyukan ci gaban dasu Amma har yanzu basu biya ba Amma dai ku sani biyan kudin ya zama wajibi akanku”

Injiniya Kutama, yace biyan irin wadannan zai taimaka waje gwamnati ta samu damar aiwatar da wasu muhimman ayyukan ci gaban kasa baki daya.

Da yake bayani akan matsalar tsaro, yace idan aka bunkasa harkokin hakar ma’adanai matsalar tsaro zata zama tarihi Yana Mai cewa hakar ma’adanai tana samawa matasa ayyukan yi masu tarin yawa a fadin kasar nan baki daya.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta haramtawa gwamnatocin jihohi karbar kudade wurin masu hakar ma’adanai inda yace babu wata jiha da take da hurumin karbar kudadan. Yace duk wani wani mai hakar ma’adanai da gwamnatin jiha ta karbi kudi a wurinsa, su gaggauta sanar da da ma’aikatar Bunkasa harkokin ma’adanai domin dawo musu da kudadansu.

 Shugaban ya jawo hankalin masu hakar ma’adanai da su tabbatar da cewa suna yin rijista da kuma sabunta rijistarsu da gwamnatin tarayya domin samun damar da gudanar da ayyukansu cikin tsari.

Leave a comment