.… Babu Sulhu Da ‘Yan Ta’adda- Gwamna Radda
Daga Shehu Yahaya
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kaddamar da rundunar Sakai wace akewa lakabi da Askawaran Zamfara, 2,646.
Da yake kaddamar da jami’an tsaron sa kai, a Gusau, gwamna Dauda ya bayyana cewa, samar da tsaro yana daga cikin kudirorin da dauka domin bunkasa ci gaban jihar Zamfara.
Yace sun yiwa al’ummar jihar alkawari a lokacin yakin neman zaben zasu taimaka wajen harkokin tsark wanda , cewarsa, “yau gashi Allah ya nufemu da kaddamar da rundunar Askawaran Zamfara wadanda da zasu taimaka ma jami’an tsaro wajan kauda “Yan Bindiga da suka addabi Jihar”
“Da yardar Allah zamuyi iya bakin kokarin mu tare da wadannan Askawaran dan ceto alumar Zamfara daga halin rashin tsaro” inji shi.
A nasa jawabin Babban bako Mai jawabi Gwamnan Jihar Katsina Diko Umar Radda, ya bayyana cewa, wannan shiri na kaddamar da ‘yan sakai dan fatatakar “Yan ta’adda shiri ne na gwamnoni bakwai na yankin Arewa Mason yamma.
Gwamna Radda yace “babu sulhu tsakanin mu da ‘yan Bindiga sai fafatawa, yanzu gwamnan Zamfara ya tarbi yankin sa nima haka wannan ya tabbatar da cewa lallai batun sulhu babu shi har abada sai munga bayin ‘yan ta’adda da yardar Allah”
Shima a nasa jabawabin Janar Ali Gusau mai murabus, ya bayyana cewa “wannan rundunar Askawaran Zamfara an samar da itane domin kare rayukan mu da dukiyoyin mu, bisa doka saboda haka zasuyi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin samun nasara aikin su”