Har Yanzu Ranar 29 Ga Watan Mayu Ce Ranar Damokuradiya_— Majalisar Dattawa

A dai dai lokacin da al’ummar kasar nan suke ci gaba da bayyana ra’ayinsu a kan matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimukuradiya a bangarer guda kuma majalisar Dattijawa ta bukaci bayyana Chief Moshood Abiola a matsayin tsohon shugaban kasa da kuma biyan sa hakkokin sa na shugaban kasa kana da bayyana sakamakon zaben 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 wanda ake cewa shi ya lashe.
Bayan tafka mahawara kan bayyana matsayin ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokiradiya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, Majalisar ta ce har yanzu ranar 29 ga watan Mayu ita ce ranar rantsar da shugaban kasa, kana babu yadda za’a dauki wani mataki irin wannan ba tare da yin doka ba.
Ko da wasu na ganin yunkurin na Majalisar Dattijan abin maraba amma masana na ganin bukatar ta su ka iya zama babbar barazana ga siyasar kasar.

Leave a comment