Yawaitar Matasa ‘Yan Sara-Suka A Kaduna Abin Takaici Ne … Dan Takarar Kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

.

An bayyana dabi’ar sare-sare da shaye shaye da wasu matasa a jihar Kaduna suka dauka wadanda ake kira da suna ‘yan Shara, da cewar abin bakin ciki ne da damuwa ga dukkanin wani mai kishin jihar Kaduna da son cigaban jama’arta.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani mai kishin jihar Kaduna da matasan yankin, kuma sanannen dan Jarida mai suna Ibrahim Ammani, lokacin wata ganawa da manema labarai da yayi a garin Kaduna.

Ibrahim Ammani wanda tuni ya bayyana aniyar shi ta tsayawa takarar dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Kawo, yace a irin wannan zamani da ake ciki na wayewa da neman ilimi abin takaici a samu wani matashi a cikin gari kamar Kaduna yana harka ta Sara suka da kwace ga jama’a.

Dan jaridar wanda ya dora laifin wannan dabi’a ta sare sare da matasan ke yi akan wasu miyagun ‘yan siyasa wadanda ke da wata muguwar manufa ta cimma burin su na shugabantar jama’a ko ta halin ka ka, ya bukaci iyayen yara da sake tashi tsaye wajen kula da tarbiyar ‘ya’yan su, ta yadda za su kasance masu amfanar jama’a anan gaba.

Ibrahim Ammani ya tabbatar da cewa idan Allah ya nufa ya zama dan majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar kawo a zaben da ke tafe, zai tsayu tsayin daka wajen inganta rayuwar matasan yankin ta hanyar sama musu ayyukan yi da guraban karo ilimi, sannan yayi kira ga jama’ar yankin na Kawo dama jihar Kaduna baki daya da su zabi cancanta a zabukan dake tafe ba yin sak ba, domin zabo masu kishin su ba ‘yan abi Yarima asha kida ba.

Leave a comment