ZABEN 2019: Isah Ashiru Ya Fice Daga Jam’iyyar APC

A yayin da zaben shekarar 2019 Mai zuwa yake karatowa, a jihar Kaduna tsohon Dan takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC a shekarar 2015 data gabata Isa Ashiru, ya bayyana cewa ya Fice Daga Jam’iyyar APC bisa abin da ya bayyana da cewa ana mulkin kama karya da rashin cika alkawurin da aka daukar wa al’ummar kasar nan.

Ashiru ya bayyana cewa yanzu ya ” Yada Kwallon Mangoro Ya huta da Kuda ”

Isha Ashiru, wanda ya bayyana haka a mazabarsa ta Kudan a karamar hukumar Kudan da ke cikin jihar Kaduna.

Dan siyasa ya bayyana cewa gwamnatin APC ta kasa cika alkawurin data daukar wa al’ummar kasar nan baki daya inda yace babu Komai da jam’iyyar tayiwa al’ummar illa yaudara da kama karya.

Ya kara da cewa a zaben 2019 Mai zuwa al’ummar kasar nan zasu canza gwamnatin APC a matakai daban-daban a fadin kasar nan baki daya.

Isa Ashiru, wanda tuni masu fashin bakin siyasa suke hasashen dama zai Fice Daga Jam’iyyar APC zai koma jam’iyyar PDP wanda kuma ake hasashen cewa zai yiwa jam’iyyar PDP takarar gwamnan a jihar Kaduna a zaben 2019 Mai zuwa.

A yayin da yake bayyana ficewarsa daga APC, Isha Ashiru, bai bayyana jam’iyyar da ya koma ba.

Jiga-jigar jam’iyyar PDP daga Kananan Hukumomin jihar Kaduna daban-daban suka halarci bikin ficewarsa daga APC.

Leave a comment