2019: Isah Ashiru Shine Mafi Cancanta Ya Zama Gwamnan Kaduna… Inji Sule Buba

An bay bayyana Isah Ashiru, a matsayin Mafi Cancanta da ya Zama Gwamnan Kaduna a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin daraktan yakin neman zaben Isha Ashiru Jakada Sule Buba, ya bayyana hakan ne a yayin da kwamitin yakin neman Isah Ashiru suka kawo Ziyara a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu na Jihar Kaduna.

Ya ci gaba da cewa Jihar Kaduna tana bukatar mutane masu son ci gaban Jihar kamar Isah Ashiru Wanda babu shakka zai kawo ci gaba a fadin Jihar.

Sule Buba ya kara da cewa “Isha Ashiru gogaggen Dan siyasa ne kuma Wanda ya San makamar shugabancin al’umma saboda idan al’ummar Jihar Kaduna suka zabe shi zasu Ga sauyin al’amura” Inji shi.

A nasa jawabin , shugaban kwamitin yada labarai na yakin neman zaben Ashiru, Malam Shu’aibu Gimi, ya bayyana cewa idan aka zabi Isah Ashiru a matsayin Gwamnan zai kyautata dangantaka a tsakanin kafafen yada labarai , hasalima, za’ayi gwamnatin kawo ci gaba a fadin Jihar Kaduna baki daya.

Leave a comment