2019: Gwamna El-Rufa’i Alherine Ga Al’ummar Jihar Kaduna -Inji Sabo Anchau

Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Kubau a jihar kaduna Alhaji Sabo Aminu Anchau, Ya bayyana gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, a matsayin Alherine ga Al’ummar jihar ganin yadda ya Fara dawo da martabar jihar a idon duniya.

Alhaji Sabo Anchau, yace shekaru uku na gwamnatin El-Rufai, tattalin arzikin jihar ya bunksa kiwon Lafiya da harkar ilimi sun inganta, Wanda Hakan Ya sanya masu zuba Jari daga kasashen duniya suka Nuna sha’awarsu wajen zuba Jarinsu a jihar kaduna.

Shugaban karamar hukumar, Ya bayyana Haka ne a wata zantawa da Yayi da manema labarai, inda yace Duk Wani me kishin jihar kaduna baiyi nadamar Zaben gwamna El-Rufai ba, hasalima, a Zaben 2019 Mai zuwa gwamnan zai ci gaba da zama Alheri ga daukacin Al’ummar jihar baki daya.

Alhaji Sabo, Wanda shine Shugaban Yakin neman Zaben El-Rufai a karamar hukumar Kubau a Zaben 2015 daya gabata, Ya bayar da tabbacin cewa kuru’un Al’ummar Karamar hukumar Kubau na Shugaba Buhari ne da Malam El-Rufai a Zaben 2019, yana Mai cewa sun gamsu da gwamnatin jihar karkashin jagorancin El-Rufai.

Ya ci gaba da cewa ” Cikin shekaru uku na gwamnatin El-Rufai mu karamar hukumar Kubau an Gina da gyara asibitocin da cikin karamar hukumar Haka kuma makarantun da suke karamar hukumar suma an Gina kuma an gyara da yawansu, Saboda Haka Ina Mai tabbatar muku da cewa jihar kaduna a Zaben 2019 ta gwamna Nasiru Ahmed El-Rufa’i ne biyo bayan ci gaba da ya Kawo jihar kaduna Wanda mu bamu Taba ganin irinsa ba”Inji shi.

Leave a comment