Gwamnatin Jihar  Kaduna Zata Hana Motocin Bas Da Tasi Aiki A Cikin Gari 

Gwamnatin jihar Kaduna ta fito da wani Sabon tsarin sufuri na zamani ta hanyar samar da manyan motocin safa-safa wadanda zasu rinka jigilar mutane a cikin kwaryar jiha wadanda zasu maye gurbin motocin Bas da Tasi.

Manyan motocin sune zasu maye motocin Bas da tasi wadanda sune suke aiki shekara da shekaru a jihar. Gwamnati ta bayyana cewa zata Samar sa manyan motocin guda 275 Wandanda tuni ta fara shigowa da su.

Tuni dai direbobin Bas da tasi sukayi watsi da Sabon shirin gwamnatin inda suka ce gwamnati na yunkirin hana su cin abicinsu ne, hasalima, gwamnati bata basu aiki ba amma zata karbe na hannunsu.

Manyan motocin sune zasu rinka aiki a titunan Ahmadu Bello da na Nnamdi Azikiwe aiki Wanda motocin Bas da Tasi zasu daina aiki a kan hanyoyin.

A cewar gwamnatin duk direban dake bukatar irin manyan motocin sai ajiye naira miliyan daya kamin ya fara aiki da motar wacce za ‘a sayarwa direbobi akan Kudi naira miliyan 48 kowacce daya.

Direbobin da suka zanta da wakilinmu, sunyi Allah wadai da manufar gwamnati ma yunkurin korarsu daga aikinsu inda sukace sama da direbobi  Dubu 10 zasu rasa aiki da zarar gwamnati ta kaddamar da motocin.

Rahotanni sun nuna cewa da yawan direbobi da yaransu sun bada gudummawa yayin zaben 2015 Wanda sunyi amfani da motocinsu kyauta a aikin zabe, wasunsu kuma da su akayi ta lika hotunan ‘yan siyasa musamman na jam’iyyar APC amma a cewarsu gwamnati ta manta hakan.

Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa akwai direbobi akalla sama da Dubu 10 a garin kaduna masu aikin matar haya baya ga yaransu Wanda sunkai Dubu 15 wadanda yanzu suke fuskantar rasa aikinsu.

Ko akwanan baya, yayin bude Sabon ofishin kungiyar NURTW na jihar kaduna, gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya jaddada kudirinsa akan Sabon tsarin sufuri inda yace babu gudu babu ja da baya akan hana bas da tasi aiki a titin Ahmadu Bello da titin Nmandi Azikiwe.

Sai rahotanni sun ruwaito cewa gwamnati tace zata sayi motocin ‘yan bas idan kudinsu Bai kai miliyan daya ba sai su bar motocin su cika da kudinsu.

A wani taro  da gwamnati ta gudanar na masu ruwa da tsaki a harkar sufiri a jihar, gwamnan jihar Nasiru El-Rufa’i, yace sabon tsarin zai kawo saukin cunkoson motocin haya a kwaryar jihar.

Direbobi sun  bayyana sabon tsarin gwamnatin a matsayin ” Zalunci da kama karya” akan direbobi.

Tuni itama kungiyar masu motocin haya NARTO tayi watsi da shirin inda tace gwamnati ba da gaske take ba, a cewarsu an budawa wasu hanyace ta sace kudin jihar.

Da wakilinmu ya tuntubi shugaban kungiyar direbobi na jihar NURTW Alhaji Alhassan 313,  Bai samu damar ganinshi ba sakamakon tafiya ummar da yayi, sai dai sakataran kungiyar Wanda yace ba zai iya cewa komai ba har sai shugabansu ya dawo.

Leave a comment