Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na Jihar Kaduna (NULGE),Kwamared Rayyanu Isyaku Turunku,ya bukaci daukakin ma’aikatan kananan hukumomin Jihar da su kasance a bakin aikin su,musamman wadanda suke kananan hukumomin Kajuru,Chikun,Kaduna ta Arewa,Kaduna ta Kudu,da Igabi, da aka sanya doka saboda rikicin da ya faru a makon jiya .
Kwamared Rayyanu Turunku ya yi wannan kiran ne a yau, a Kaduna,a lokacin da yake tattaunawa dà manema labarai a Kaduna .
Ya ce tun da zaman lafiya ya fara dawowa wandà a sabili da ganin haka ya sa gwamnatin Jihar Kaduna ta sassàuta doka ya koma daga karfe 6:00am zuwa karfe 5:00pm,ya sa ya yi wannan kiran .
Shugaban iya ce muddin gwamnati ta ga al’ummar jihar sun yarda, sun rugumi juna, sun yarda su zauna lafiya,to za ta rika sassauta dokar har ta cire shi gaba daya .
Ya yaba wa ma’aikatan kananan hukumomin saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da rikicin bai yadu ba a sauran daukakin kananan hukumomin jihar 23,sannan sun kuma sun yi kokari zaman lafiya ya fara dawowa yadda ya kamata .
Haka ya jinjina wa gwamnan Jihar Kaduna,Mallam Nasir Ahmed El-Rufa’i saboda matakan gaggawa da ya dauka a lokacin da rikicin ya barke .
Sannan ya bukaci al’ummar Jihar Kaduna da su rungumi akidar zaman lafiya domin samun ci gaba .
Haka ya ce a halin rashin zaman lafiya babu wani ci gabà da za a samu sai koma baya .