Gwamnatin Tarayya Ta Karbo Basuka Na Fiye Da Naira  Tiriliyan Daya  A Cikin Shekaru 8 

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa  ta samu nasarar karbo basuka na fiye da Naira Tiriliyan guda cikin shekaru 8, ta hannun hukumar dake kula da kadarorin g

wamnati.

Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ce, ta bayyana hakan a yayin da take kaddamar da darkatocin hukumar ta AMCON a baban birnin Tarayya Abuja karkashin jagorancin Mr Muiz Banire mai darajar SAN.

Hajiya Zainab ta ce tun bayan kaddamar da hukumar ta AMCON a shekara ta 2010, hukumar ta sami nasarar karbo basuka na fiye da Tiriliyan guda daga masu cin bashi daga bankuna da halin yanzu suke fuskantar zargin cin hanci da rashawa.

Ministan ta kara da cewar, gwamnatin tarayya ce ta kafa hukumar ta hannun babban bankin kasa CBN, don ceto bankuna daga neman durkushewa, bayyan da wasu tsirarun mutane suka ci, amma suka kasa biya.

Leave a comment