TSARO A ZAMFARA: Jami’an Tsaro Sun Damke Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Anka

Jami’an tsaro na musamman da ke yaki da mahara a jihar zamfara mai suna ” Operation Sharan Daji” sun damke mataimakin shugaban karamar hukumar Anka da ke jihar Yahuza Ibrahim Wuya bisa zarginshi da hannu dumu-dumu wajen taimakawa maharan da suke kashe mutane a yankin.

An damke Ibrahim Wuya ne a ranar 13 ga watan Afrilun nan biyo bayan bayan sirri da suka nuna cewa shi Wuya yana bawa maharan bayanan sirri akan masu aikin sa kai a jihar, hasalima shime yake saida musu da shanun da suke karba a hannun mutane.

Haka kuma jami’an tsaron sunce Ibrahim, shine ya jagoranci belin wani gawurtaccen Dan ta’addar nan mai suna Sani Yaro daga cikin Yarin Gusau.

A wata takardar sanarwa da mai kula da yada labarai na jami’an SHARAN DAJI, Manjo Clement Abiade, yace zasu mika Yakubu zuwa ga hannun hukumomin tsaron da suka kamata domin yanke masa hukuncin da ya kamata bayan sun kara yin bincike akan shi.

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Leave a comment