Hukumar FRSC Zata Fara Gwajin Kwakwalwa Ga Masu Tukin Ganganci

Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa FRSC ta bayyana cewa daga yazu duk wanda ta kama yana tukin da ya kauce tsari to babu shakka sai an yi masa gwajin kwakwalwa.

Kwamandan rundunar reshen jihar Ogun Clement Olalede ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Ota.

A cewar sa dukkanin matukin da aka kama na kauce hanya ko kuma yana yin tuki ba yadda aka tsara ba musamman ma a yayin bukukuwan ista da ke karatowa, to za a tuhumeshi da laifin tukin ganganci.

Kwamandan ya ce irin wadan nan direbobo masu kunnen kashi, bayan wancan gwaje-gwajen na hauka za kuma su biya tarar naira dubu 50 ko kuma dauri a gidan yari.
Mr Oladele ya kara da cewa tuni hukumar ta fara shawagi a hanyoyin kasar nan, bisa karatowar biki Easter domin rage matsalolin da ake fuskanta a kan hanyoyin kasar nan.

Leave a comment