Babu Gwamnan Dake Son Zaman Lafiya Kamar El-Rufai – Cafra Caino

Shugaban karamar hukumar Kajuru, Honarabul Cafra Caino, ya bukaci Al’ummar karamar hukumar Kajuru, su ci gaba da kasance masu son zaman lafiya da kaunar juna, kamar yadda tarihi ya sansu da shi.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a kaduna. Honarabul Cafra Caino, ya ci gaba da bayyana cewa, “Kowa yasan mutanen Kajuru, mutane ne masu son zaman lafiya da mutunta juna, ba tare da nuna ban bancin addini ko kabilanci ba, sannan Allah ya albarkaci karamar hukumar Kajuru da dimbin abubuwan Alheri da na tarihi, wanda duk fadin Afrika ana zuwa domin yawon bude ido karamar hukumar Kajuru.”

A cewarsa, “Abin da ya faru a Dan kwanakin baya, lamari ne na halin Shaidan, wanda ya yi amfani da wasu daga ciki marasa kishin kansu, karamar hukumarsu, kuma da Al’ummarsu, har ya ci nasarar su da hakan. Amma da izinin Allah, ina mai tabbatar maku da cewa hakan ba zai sake afkuwa ba”

Ya kara da cewar, “Amma a halin yanzu zaman lafiya ya dawo kamar yadda aka sani a karamar hukumar Kajuru, da taimakon Allah, da taimakon jajirtattacen Gwamnanmu na Jihar kaduna.”

Honarabul Cafra Caino, ya kuma shawarci Matasan karamar hukumar Kajuru, da su ci gaba da kasancewa zaman lafiya da juna, sun guji kaukar ko wane irin doka a hannu, sannan su tabbatar suna kai rahoton duk wani batagarin Mutum ko na kungiyoyi wadanda basu yarda da su ba, ga jami’an tsaro.

Daga karshe, Shugaban karamar hukumar na Kajuru, Mista Cafra Caino, ya jinjina ma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai, a matsayinsa na wanda yafi kowa son a zauna lafya, da kuma irin gudummuwa na abubuwan ci gaban more rayuwa da yake kawo ma Al’ummar karamar hukumar Kajuru. A cewarsa, ya zama wajibi su ya bama Mai Girma Gwamnan dangane da hakan.

Daga Ibrahim Khalil, Kaduna

Leave a comment