Burina Ya Cika, ‘Dana Ya Fara Karatu A Makarantar Gwamnati -El-Rufa’i

Daga Shehu Yahaya, kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed el- rufai, ya cika alkawarin da ya dauka na sanya ‘ya’yanshi makarantar gwamnatin kamar yadda sauran ‘ya’yan talakwa Suke zuwa.

Gwamna El-Rufa’i wanda ya kai ‘Dan shi mai suna Abubakar Al-Siddique El-Rufa’i, mai shekaru 6 da haihuwa makarantar gwamnati ta “Kaduna Capital School ” dake Malali dake karamar hukumar kaduna ta Arewa.
El-Rufai,wanda shine gwamna na farko a Arewacin kasar nan da ya kai ‘Danshi makarantar gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa yanzu burinshi ya cika kuma ya cika alkawarin da ya dauka cewa idan ‘Danshi ya kai shekaru 6 zai sanya shi makarantar gwamnati yana mai cewa ” wannan shekarar ‘Dana ya cika shekara 6 cur saboda yau da kaina a matsayin na mahaifi na kai ‘Dana ayi mishi rijistar shiga aji daya na Firamare” Inji shi.

Leave a comment