Gurbatattun ‘Yan Siyasa Ke Shirin Wargaza Jihar Zamfara – Inji Matawalle

Daga Auwalu Tanko

Gwamnatin Jihar Zamfara ta fallasa cewa ta samu ‘rahotanni na sirri’ dangane da wani kulle-kullen da wasu ‘yan siyasa ke yi domin su ‘tarwatsa’ Jihar Zamfara.

Sai dai kuma gwamnatin jihar wadda PDP ce ke mulkin ta, ba ta bayyana sunayen wadanda ta ke zargi da wannan shirin da ta kira na tarwatsa jihar Zamfara din ba.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Zamfara ya fitar, Yusuf Gusau ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa “na kulle-kulle tare da hadin baki da Boko Haram domin a rika kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba hare-hare.”

Jami’in ya kara da cewa shirin da wadannan marasa kishi ke yi shi ne domin su lalata sulhun zaman lafiyar da aka cimma a jihar ta Zamfara.
Daga nan ya kara da cewa “wadannan masu wannan mugun nufi sun yi shirin kai hare-hare a kananan hukumomi bakwai na cikin jihar da kuma wasu wurare muhimmai da ke cikin Gusau, babban birnin jihar.”

Sanarwar ta kuma kara da cewa masu wannan shiri sun shirya “bindige wasu mashahuran mutane biyu na cikin jihar.”

“Kananan hukumomin da suka shirya kai wa hare-hare sun hada da Gusau, Tsafe, Talata Mafara, Anka, Zurmi, Maru da Maradun. Wurare biyu da suka shirya kai hari a Gusau su ne Babban Masallacin Juma’a na garin da kuma kasuwar cikin bariki, wato Gusau Mammy Market.’

“An ce tuni sun dauki sojojin haya ‘yan Boko Haram da za su rika kai wadannan hare-hare, tsakanin ranar Litinin, 23 Ga Satumba, zuwa 25 Ga Oktoba, 2019.” Inji sanarwar.

Daga nan sanarwar ta ce wannan barazana ba za ta tauye wa Gwamna Bello Matawalle guiwar ci gaba da samar da tsaro a fadin jihar ba.
Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da direbobin motoci da na baburan acaba su rika kula sosai da wadanda za su rika dauka.

Gwamnan ya kuma nuna jin dadin yadda mahara su sake sakin wasu mutane 30 da suka hada da maza 15, mata 15.

Leave a comment