Mataimakiyar Gwamnan Kaduna Ta Nisanta Kanta   Akan Masu Amfani Da Sunanta A Shafukan FACEBOOK 

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

Mataimakiyar Gwamnan jihar kaduna Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ta nisanta kanta akan masu Amfani da sunanta a shafukan sada zumunta na zamani FACEBOOK suna yada labaran karya a kanta.

A wata Sanarwa da Hadiza Sabuwa, ta fitar wanda matamakinta Akan Shafukan Sada zumunta Peter Ibrahim, ya wallafa shafinsa na FACEBOOK, Ta nuna damuwarta dangane da yadda wasu ‘Yan siyasa marasa aikinyi suke amfani da sunanta a shafukan sada zumunta na zamani suna wallafa bayanai da sunanta kamar haka “Hadiza Balarabe”

Sanarwar tace ” Ina Jan hankalin al’umma akan wasu bayanai da wasu suke amfani da sunana a shafukan sada zumunta na FACEBOOK suna sanya wasu kalamai a matsayin nine nake wallafasu”

Akan tace duk wanda aka kama yana ci gaba da amfani da sunanta zai fuskanci fushin hukuma.

Leave a comment