Sanya ‘Dan El-rufa’i Makarantar Gwamnati Yaudara Ce — Shehu Sani

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisa ta takawas, Shehu Sani yayi martani a kan sanya Abubakar makarantar gwamnati da Gwamna Nasir El-Rufai.

Sani ya ce gwamnan yayi amfani ne da salon yaudara a siyasance domin yaudarar al’ummomin dake wajen Kaduna kasancewar ba su san yadda makarantun gwamnatin jihar suka lalace ba.

Ya kuma bayyana wannan aiki a matsayin wasan kwaikwayon Kannywood ko kuma Nollywood, ba komi ya sanya shi wannan abu ba, banda zabe mai zuwa na 2023.

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, Shehu Sani ya ce: “Babu komi cikin wannan al’amari in banda siyasa domin ya janyo hankali jama’a ta hanyoyin sada zumunta musamman wadanda ba mazauna garin Kaduna.

“Ba wai adawa nake yiwa gwamnan ba, amma duk wanda yake zaune a garin Kaduna ya san abinda gwamnan yayi wasan kwaikwayone kawai.

Wasan Kannywood kawai gwamnan yayi da jama’a domin ya gyara siyasarsa a saboda zabe mai zuwa. “Babu yadda mutum zai kashe miliyan N195 a kan makaranta guda daya sannan ya kai yaronsa ku yi tunanin abin yabo yayi.

Kamata yayi ya mayar da hankali wurin gyaran makarantun gwamnatin jihar. “Akwai tsoffin gwamnonin jihar nan kamar Balarabe Musa wanda bai taba zama a gidan gwamnati ba har ya gama mulkinsa.

Haka kuma akwai Ahmed Makarfi wanda zan iya tunawa yaransa sun yi wannan makarantar da El-Rufai ya sa yaronsa. “Indai wasan kwaikwayone ba yau El-Rufai ya soma ba.

Akwai lokacin da aka dauki hotunansa yana bin masu satar mutane a kan hanyar Abuja. Don haka halayen El-Rufai indai da sabo mun riga mun saba yanzu.” Inji Shehu Sani.

Leave a comment